Bayanai 21 masu ban sha’awa da baku sani ba game da Sani Abacha

Yau shekara 21 ke nan kenan da rasuwar Janar Sani Abacha kuma tarihin Nijeriya bai cika ba ba tare da ambaton Sani Abacha ba. Shugaban Kasa na 7 na Najeriya, Sani Abacha ya mutu a ranar 8 ga Yuni, 1998, yayin da yake fadar Shugaban kasa, Abuja. An kuma kawo shi Kano an binne shi a wannan rana, bisa ga ka’idodin addinin Musulunci, ba tare da an yi gwaje gwaje a kansa ba. Wannan ya haifar da jita-jita cewa watakila an kashe shi da niyya ta hanyar abokan hamayyar siyasa ta hanyar sa masa guba.

Yanzu, bari in kawo muku wannan tabbatattun bayanai guda ashirin da daya da baku sani ba game da Janar Sani Abacha:

 1. An haifi Janar Sani Abacha ne a ranar Litinin, 20 ga Satumba, 1943, a Kano, kuma ya mutu aka binne shi a ranar Litinin, 8 ga Yuni, 1998. Asalinsa Kanuri ne daga Jihar Borno.
 2. Ya auri Shuwa Arab, Maryam, kuma daga jihar Borno, a shekarar 1965 kuma tare suna da yara maza shida da mata uku. Yaron farko, Ibrahim, ya mutu a hadarin jirgin sama a shekarar 1996.
 3. Dan sa na karshe an haife shi a Aso Rock a 1994 lokacin da Abacha ya cika shekaru 50 da matarsa Maryam mai shekaru 47. Yaron an sa masa suna Mustapha,
 4. Abacha shi ne shugaban soja na farko da bai ya taba tsallaken Mukamin Soja ba don zama cikakken janar-janar.
 5. Janar Abacha shine kamar yadda wasu bayanai ke nunawa Janar Mafi Nasara nasarar juyin mulki a tarihin Najeriya. Marigayi janar ya taka rawa a kowane juyin mulki mai nasara da aka gudanar a cikin kasar kuma ya taimaka matuka wajen kawo tare da cire Manjo-Janar Muhammadu Buhari daga mulki a 1983 da 1985.
 6. Abacha ya sanar da juyin mulkin da ya kawo karshen gwamnatin Shugaba Shehu Shagari a ranar 31 ga Disamba, 1983, wanda daga karshe ya kawo Manjo-Janar Muhammadu Buhari kan karagar mulki. Hakanan, bayan kifar da Buhari a ranar 27 ga Agusta, 1985, Abacha ne ya sanar da babban hafsan sojojin, Manjo-Janar Ibrahim Babangida, a matsayin sabon shugaban mulkin soja kuma babban kwamandan sojoji, Brigadier Joshua Nimyel Dogonyaro ne ya karanta jawabin (juyin mulkin).
 7. Jahar Abacha mutum ne marar surutu dayawa.
 8. A hukumance, bai kifar da gwamnatin rikon kwarya ba a shekara ta 1993. Shugaban gwamnati, Cif Ernest Shonekan, ya yi murabus sannan Abacha a matsayin sakataren tsaro kuma babban jigon gwamnati ya karɓa, a takaice, juyin mulki ne ba tare da zubar da jini ba.
 9. Biyu daga cikin mahimman shawarwarin taron kundin tsarin mulkin 1995 da ya kafa sune ware 13% ga yankunan da ake hako mai da kuma shiyyoyi shida na kasar nan.
 10. Janar Abacha bai taba rike mukamin da ba na soja ba har zuwa lokacin da ya zama ministan tsaro a 1990 (daga baya an canza zuwa sakataren tsaro a shekarar 1993). Yana Lieutenant-Janar ne a lokacin.
 11. Magoya bayan Janar Abacha sun bayyana shi a matsayin mai kula da tattalin arziki, kuma ya daidaita musayar kudi akan N22 / $ 1 amma duk da a bayan fage N80/$1. Wannan shine ya haifar da yawan neman haya, tare da yawancin ‘zaɓaɓɓun’ abokai ko shafaffu da mai suna saya a kan farashin gwamnati wanda kuma farashin kasuwannin bayan fage suka ninka shi har sau huɗu.
 12. janar Abacha ya kara farashin mai sau daya a cikin shekaru hudu da rabi a kan karagar mulki sannan ya kafa Asusun Kula da Man Fetur (Na Musamman), wanda aka yarda da shi sosai cikin ayyukan ci gaban kasa da harkar ilimi, kiwon lafiya, da ruwan Sha.
 13. Matarsa, Maryam ce ta fara kafa abin da yanzu ake kira da Babban Asibitin Kasa, Abuja. (National Hospital) kuma ya samo asali ne daga Asibitin Kasa na Mata da Yara kafin a inganta shi a cikin abin da ke shirin zama babban asibitin gwamnati na Najeriya mai lamba daya.
 14. A karkashin mulkin Janar Abacha ne Najeriya ta zama mai shigo da Tacaccen Man Fetur ba ji ba gani, sabo da an juya wa matatun mai baya. Shekaru 20 bayan rasuwarsa, Najeriya har yanzu ta dogara kacokam kan shigo da mai.
 15. Wani abin da ba a iya mantawa da shi ba a ƙarƙashin Janar Abacha shi ne shigo da wani nauin mai” Man Danko” wanda yake da Wari kuma yake lalata injunan mota.
 16. Sani Abacha ya taimaka wajen maido da zaman lafiya da dimokiradiyya a Saliyo da Laberiya bayan yakin basasa na shekaru.
 17. A cikin 1995, bayan kashe Ken Saro-Wiwa, mujallar Time, ta kira Janar Abacha da sunan “Thug of the Year.” A cikin 2004, a cikin 2004, Abacha ya kasance mutum na huɗu da ya fi cin hanci da rashawa a tarihi.
 18. Janar Abacha bai cika bayyana a bainar jama’a ba, ba ya kuma amsa tambayoyi ko ba da damar buga kowane bayani game da shi, kuma ya na kuma da dabi’ar yin aiki da daddare kawai.
 19. Janar Sani Abacha ya kasance mafi Gajarta Shugabanin Kasar Najeriya a tarihi. Yana da tsawn ƙafa 5, da inci 7.
 20. dalilin Mutuwar Abacha har yanzu na dabaibaye a cikin asiri, wasu na zargin an kashe shine don canza akalar siyasar kasar.
 21. Abin mamakin shi ne, gwamnatin Najeriya har yanzu tana karbo kudaden da wai ake zargin ya kwashe ya kai asusun ajiyar kasashen waje a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: