Muhammadu Ribadu: Ministan Tsaro na Farko a Nigeria

Bayan samun yanci, Ministan Tsaro na farko a Najeriya shine Alhaji Muhammadu Ribadu (1910-1965).
Ministan tsaron Najeriya babban ma’aikaci ne a majalisar zartarwa ta tarayyar Najeriya wanda ke kula da ma’aikatar tsaron Najeriya. Babban aikin Ministan Tsaron shi ne gudanar da dukkan rassan Sojojin Tarayyar Najeriya, da kiyaye rundunar soji ta zamani, wacce zata tabbatar da kwararrun Soja wanda suka cancanta, kuma don kare yankin kasa na Tudu, Tekuna da Kuma Sararin Samaniya. na Tarayyar Jamhuriyar Nijeriya.

An haifi Alhaji Ribadu a Bulala, wanda a halin yanzu ta ke jihar Adamawa. Ya yi fice a fagen Siyasa a Yankin Arewa kuma ya shiga Majalisar Wakilai ta Arewa a Kaduna a 1947.
Ta haka ne ya fara shiga Fagen siyasa wanda kuma ba da daɗewa ba ya zama jagora a cikin Kungiyar Jama’a ta Arewa (NPC), wanda aka kafa a 1949 a matsayin ƙungiyar al’adu amma ba da daɗewa ba ya juya zuwa jam’iyyar siyasa don biyan bukatun Kundin Tsarin Mulkin Macpherson.

A karkashin jagorancin Sardauna na Sakkwato, Alhaji (Sir) Ahmadu Bello (1909- 1966), dan siyasa mafi karfi a lokacin mulkinsa, NPC ta lashe dukkanin kujerun Arewa a zabukan farko na Najeriya a 1951-52 kuma Alhaji Muhammadu Ribadu ya kasance daya daga cikin ‘yan takarar Arewa da ya ci zaben Majalisar Wakilai ta Tarayya da ke Legas inda aka nada shi Ministan Albarkatun kasa. A baya ya kasance darakta a Kamfanin Kasuwancin Kayayyakin Najeriya, amma ya yi murabus a wannan mukamin na zama Ministan.

A shekarar 1954, an nada shi Ministan Albarkatun kasa da Makamashi; ya yi aiki a wannan ma’aikatar har zuwa 1957 lokacin da aka sauya shi zuwa Ma’aikatar kula da Alamuran Legas. Ya kasance Mataimakin Shugaban Na NPC na biyu, kuma daga cikin shugabannin da suka yi fice a cikin tsarin NPC da ta mamaye yawancin Majalisar Tarayyar Najeriya.
Ya karbi Lambar Girma ta Member na Masarautar Burtaniya (MBE) a 1952.
Yayin da ya ke Ministan Tsaro, Ribadu ya shugabanci aikin fadada rundunar Sojojin Najeriya, Navy da kuma kirkirar Sojojin Sama. Ya kafa Kamfanin Masana’antu na Tsaro a Kaduna, da Kwalejin Tsaro ta Najeriya a Kaduna da kuma Second Recce Squadron a Abeokuta.

Babu shakka, Alhaji Ribadu babban mutum ne. a cikin Manyan mutane. Yana cikin kusa komai na al’amarin mulki, Mataimakin Firayim Minista. Ya kasance mai karfin iko. Abokan aikinsa sukan kira shi da “ikon iko”. Ya kammala aikin Tsarawa da Zamanantar da Sojojin Najeriya. Har zuwa yau, ana ci gaba da tuna shi a matsayin daya daga cikin fitattun Ministocin Tsaron Najeriya da ya taba yin irinsa ba.

Masana tarihi sun yi imanin cewa da Ribadu yana raye, juyin mulkin 15 ga Janairu, 1966 ba zai faru ba.
A ranar 1 ga Mayu, 1965, an shirya baiwa Muhammadu Ribadu, Firayim Minista, a lokacin Alhaji (Sir) Abubakar Tafawa Balewa (1912-1966) tare da Fifimiyan Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello suka samu lambar yabo ta zinare ta Usmamiya order a Kaduna. amma ya mutu da safiyar ranar a lokacin yana da shekara 55.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: